Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canje-Canje Da Duniya Ke Samu Nada Alaka Da Yanayin Mutane


Kimanin shekaru billiyan 4.5 kenan da suka wuce, yanayin duniya yana canzawa sosai matuka. Duniya kan fuskanci wasu canji masu kyau da ma’ana a wasu kuma lokkuta akan samu akasin hakan.

Ko a yau za’a iya ganin cewar abubuwa na canzawa a fadin duniya, wanda wasu daga ciki sukan faru ne haka nan, kamar yadda Allah yaso wasu kuwa sukan faru ne a sanadiyyar tallafi na dan’adam. Wadannan canje-canjen sukan faru ne a sanadiyar yadda yanayi ke canzawa, da yadda koguna ke kafewa ko gudana, haka da girgizar kasa, ambaliyan ruwa, da matsanancin zafi ko sanyi a fadin duniya. A jihar Alaska ta Amurka da akasanta da mashahurin sanyi, suma sun fara samun yanayin zafi wanda ya wuce kima, wanda kimanin shekaru 50 da suka wuce ba’a samun irin wannan zafin a yankin.

Masana na ganin cewar duk hakan na faruwa ne a sanadiyyar yadda mutane ke bada tasu gudunmawa, ko dai mutane na hawa abubuwan hawa da basu da isashiyar lafiya, ko kuma mutane basu zubar da shara yadda ya kamata, da ma yadda mutane ke gudanar da mu’amalar su ta yau da kullun, haka yin gine gine a hanyoyin wucewar ruwa na haifar da illoli da dama ga rayuwar bil'adam. Akwai bukatar mutane su fara maida hankali wajen ganin sun taimaka wajen ganin an magance matsalar dumaman yanayi a duniya, a kuma kowane yanki suke.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG