Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyar Zasu Fafata a Neman Shugabancin FIFA


FIFA President
FIFA President

Kwamitin gudanar da zabe na Hukumar wasan kwallo kafa ta duniya wato (FIFA) ta fitar da sunayen mutane biyar wadanda zasu fafata a zaben neman shugabancin hukumar wanda za’a gudanar ranar 26, ga watan Fabrairu 2016.

Masu fafatawar sun hada da Yarima Ali Bin Al-Hussein, na kasar Jordan, Sheik Salmam Bin Ibrahim Al-Khalifa, daga Baharain da Jerome Champagne na kasar Faransa.

Akwai Gianni Infantino, daga Italiya, da kuma Tokyo Sexwale daga Afirka ta kudu.

XS
SM
MD
LG