Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ga Jaddawalin UEFA Zagaye Na Gaba


An fidda jaddawalin zagaye na gaba (Round of Sixteen) na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, Uefa Champions league, na shekara 2017/18

Ga yadda wasannin zasu kasance

Kungiyar Juventus da Tottenham, FC Basel da Manchester City, Sevilla da Manchester United, Real Madrid da Paris Saint-Germain, Chelsea da Barcelona, Bayern Munich da Besiktas, FC Porto da Liverpool.

Za'a fara wasanni hudu na farko ranar Talata 13 ga watan Fabarairu, 2018 da kuma Laraba 14 ga wata, sai kuma satin gaba a fafata a sauran wasanin.

Za'a buga wasan kusa da na kusa da na karshe (Quarter Final) a ranar Jumma'a 16 ga watan Mayu, 2018, tsakanin kungiyoyin da suka samu nasara a zagaye na 16.

Wasannin da sukafi daukar hankali sune tsakanin Real Madrid da Paris Saint-Germain, Chelsea da Barcelona, sai kuma Sevilla da Manchester United.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:28 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG