Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Kujerar Shugbancin Hukumar FIFA Na Neman a Dage Zaben Hukumar


Dan takarar kujerar shugaban hukumar kwallon kafar FIFA Ali bin al-Hussein, ya yi kira da a dakatar da zaben da aka shirya za a yi ranar Jumma’a saboda wata rashin jituwa da aka samu akan shirin yadda za a yi zaben.

Lauyan da ke kare yariman na kasar Jordan ya ce za su daukaka kara a kotun ‘yan wasa bayan da hukumar ta ki amincewa da bukatar yarima Ali ta a samar da runfunan zaben da za a iya ganin abinda ke wakana daga waje.

Yariman ya bukaci a kafa rumfunan zaben da za a iya ganin abun da ke faruwa daga waje don tabbatar da cewa wakilan da ake matsawa lamba akan su zabi wani dan takara ba su dauki hoton kuri’un su ba don nunawa dantakarar cewa ga yadda su ka yi zabe. Jami’an hukumar FIFA sun ce ba za su bari wakilan su shiga wurin zaben da wayar hannu ba.

‘Yan takarar 5 ne ke neman maye gurbin kujerar Sepp Blatter, shugaban hukumar FIFA da ya fi dadewa, wanda aka tilastawa sauka kan kujerar cikin shekarar da gabata saboda wasu rigingimu da suka taso.

XS
SM
MD
LG