Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Dai Kamfanin Apple Yaki Bude Wayar Syed


Apple IPhone 6
Apple IPhone 6

Wani sabon binciken jin ra’ayin mutane da akayi a nan Amurka, na nunin yawancin Amurkawa na goyon bayan matakin da jami’an tsaron Amurkar ke dauka na ganin sun takurawa kamfanin Apple, da ya samar da hanyar zasu iya bincikar wayar ‘daya daga cikin mutanen da suka kai hari garin San Bernardino dake California.

Cibiyar bincike ta Pew Research, tace ta nemi jin ra’ayoyin mutane sama da Dubu, cikin yan kwanakin nan inda ta gano cewa sama da kashi 51 cikin 100 na mutanen, na ganin ya kamata kamfanin Apple ya bude wayar iphone mallakar Syed Rizwan Farook, kaso 38 cikin 100 kuma na goyon bayan matsayar kamfanin na hawa kujerar naki. Kaso 11 kuma basu da wani ra’ayi kan batun.

A halin yanzu kuma, lauyan iyalai 14 da farook ya kashe yace ba da dadewa ba zai fitar da wasu bayanai da zasu goyi bayan hukuncin da alkali ya yanke, na cewa Apple ya bude wata hanya da zata baiwa jami’an tsaro damar bincikar wayar. Farook dai Amurka ne wanda shi da matarsa ‘yar asalin Pakistan Tashfeen Malik suka kai hari da kashe mutanen.

Apple dai na ci gaba da zaman kan kujerar naki kan hukuncin da kotu ta bayar.

A jiya Litinin ne shugaban Apple Tim Cook, ke gayawa masu amfani da kayan kamfanin cewa wannan bukata ta gwamnatin Amurka na da sarkakiya.

XS
SM
MD
LG