Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin "Drone" Mai Yawo A Ruwa Na Farko Da Aka Kirkira A Duniya


Jirgin Ruwa
Jirgin Ruwa

Rundunar sojojin Amurka, a karon farko sun kirkiri wani katafaren jirgi mai yawo cikin karkashin ruwa wanda ake kira “Drone” a turance. Mafi akasarin drone da aka sani suna yawo ne a sararin samaniya, inda mutun zai rike abun da zai dinga juya shi yadda yake so. Amma sai gashi an kirkiri wani mai yawo a cikin ruwa. Shi dai wannan jirgin shine na farko a fadin duniya da aka taba kirkira, yana da tsawon mita 130. A cewar mataimakin hukumar kula da sojojin kasar Mr. Walke, yace wannan jirgin yana iya yawo a cikin ruwa batare da wani ya taba shi ba.

Rundunar sojojin ruwa ta Amurka zasu dauki nauyin kula da wannan jirgin, na tsawon watanni 18, daga farkon watan Afrilu, ya kara da cewar za suyi amfani da wannan jirigin, wajen tsare kasar su daga makiya, da kuma samar da matakan tsaro ga kasar. Da dama dai akanyi amfani da wannan na'urar wajen leken asiri.

Shi dai jirgin zai iya yin aiki har na tsawon kwanaki 60 zuwa 90 batare da ya tsaya ba. Gwamnatin kasar dai ta ware kimanin dallar Amurka $3B billiyan don kara gano hanyoyi da za’a inganta kimiyyar jirgin, a tsawon shekara daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG