Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colombia Ta Lallasa Kasar Brazil


Germany Soccer Champions League Final
Germany Soccer Champions League Final

Dan wasan Brazil Neymar yace, laifin alkalin wasa za’a gani da ya dakatar da shi bayan da Colombia ta lashe wasansu inda tayiwa kasar sa ci ‘daya mai ban haushi a gasar wasan Copa America.

Jesion Murillo ne kadai ya sami damar zarga kwallo cikin raga a wasan na mintuna casa’in, an ‘dagawa Neymar jan kati bayan da aka tashi daga wasa a dalilin gware da yayi da ‘dan wasan Colombia. Alkalin wasa Enrique Osses ne ya daga Katinan har biyu ga ‘dan wasan gaba na Barcelona da kuma Carlos Bacca.

Alokacin da yake magana gidan talabishin na SporTV Neymar yace, “doka kullum akaina take karewa, ba wanda aka baiwa sai ni. Alokacin kwallon na hannuna ne, kuma ba da niyya nayi ba.” ya ci gaba da cewa irin wannan na faruwa, idan aka saka alkalin wasa da bai kware ba. wannan abu na damuna, ina jin haushi idan na hadu da alkalin wasan da bayayin abinda ya kamata.

Neymar dai zai rasa wasan karshe na rukunin da Brazil zata buga da kasar Venezuela ranar Lahdi idan Allah ya kaimu, amma wannan dakatarwar da akayi masa sai kwamitin ladabtarwa sun zauna sun kuma amince da ita.

XS
SM
MD
LG