Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Carl Ikeme Ya Bayyana Dalilin Sa Na Yin Murabus


Mai tsaron gidan kungiyar kallon kafa ta Wolverhampton Wanderers, Carl Ikeme, wanda kuma shine tsohon mai tsaron gidan kungiyar Super Eagles ta Najeriya.

Carl Ikeme, mai Shekaru 32 da haihuwa ya bayyana dalilin da yasa yayi Murabus, inda yace dole ce ta tilasta ma sa yin hakan dalilin ciwon da yake fama dashi.

Dan wasan na fama da ciwon da ake kira da cutar (acute Leaukaemia) wato ciwon daji na jini, yayin da likitocin sa suka bashi shawara da yayi murabus domin ya zauna ya nemi lafiya.

An same shi da ciwon daji tun shekara ta 2017, Carl Ikeme ya kara da cewa yabar kallon ne domin lafiyar sa ita ce muhimmiyar abu a rayuwar sa, don haka ne yayi murabus domin ya koma gida ya kula da lafiyar sa da kuma kasacewa tare da iyalin sa.

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG