Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsenal Ta Sha Da Kyar A Singapore


Mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafar Atletico Madrid Antonio Adan, ya taimakama kungiyar wajen kareta daga samun bugun daga kai sai mai tsaron gida ‘Penaltiy’ kana ya bada kwallo da ta kaiga nasarar lashe wasan. Wanda haka ya kai kungiyar Arsenal rasa kofinta na kawancen kasa-da-kasa.

Mai tsaron gidan mai shekaru 31, wanda ya taka rawa a kasar Singapore biyo bayan sa hannu a kwantiraki da yayi. Shi kuwa dan wasa Emile Smith-Rowe ya taka rawa wajen ganin dan wasa Luciano Vietto bai samu sakat ba.

Amma ‘yan wasa kamar su Henrikh Mkhitaryan da Joseph Willock, da Edward Nketiah, duk sun sha kashi a wajen dan wasa Adan wanda hakan ya ba kungiyar nasarar saka kwallaye 3 da 1 da suka samu a bugun daga kai sai mai tsaron gida, kungiyar Arsenal ita ke kan gaba a inda sauran kungiyoyin ke biye.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG