Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Fitar Da Sunayen 'Yan Wasa Da Kwac-Kwac Da Zasu Kara


A ranar talata 24/7/2018 hukumar dake kula da wasan kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta fidda jerin sunayen yanwasan kwallon kafa Maza guda 10 wadan da zasu kara a takarar zama zakaran kwallon Kafa na Duniya a shekara 2018.

Ga sunayen kamar haka

Akwai Cristiano Ronaldo wanda ya koma Juventus, daga Real Madrid dan kasar Portugal, shine mai rike da kambun a yanzu.

Kevin De Bruyne daga Manchester City a kasar Belgium

Antoine Griezmann na Atletico Madrid dan kasar Faransa

Eden Hazard – Dan asalin Belgium mai bugawa Chelsea wasa

Harry Kane – Daga Ingila, mai bugawa Tottenham wasa.

Kylian Mbappe na Paris St-Germain daga kasar Faransa kuma shine ya lashe Kyautar matashin dan wasa a gasar cin kofin duniya 2018.

Lionel Messi na kungiyar Barcelona daga kasar Argentina

Luka Modric daga Real Madrid dan asalin kasar Croatia

Mohamed Salah - Liverpool daga Misira

Raphael Varane - Real Madrid daga Faransa

bayan haka hukumar ta bayyana sunayen masu horas da ‘yan wasa a bangaren Maza guda 11 wadanda zasu fafata suma wajan zaben gwarzon Koci a tsakaninsu. Kwacakwacan sune kamar haka;

Massimiliano Allegri dan kasar Italiya mai horas da kungiyar Juventus,

Stanislav Cherchesov dan kasar Rasha, shi ne Kocin Rasha,

Zlatko Dalic (Croatia) mai horas da Croatia,

Didier Deschamps (Faransa) wanda ya jagoranci kasar ta lashe kofin duniya karo na biyu a kasar Rasha.

Pep Guardiola dan kasar(Spain ) na Manchester City,

Jurgen Klopp (Jamus) Kocin Liverpool,

Roberto Martinez (Spain) da Belgium,

Diego Simeone (Argentina) - da kungiyar Atletico Madrid,

Gareth Southgate (Ingila) Kocin Ingila ,

Ernesto Valverde (Spain) kocin Barcelona,

Zinedine Zidane dan kasar (Faransa) wanda ya jagoranci kungiyar Real Madrid,

Za a kammala zaben a ranar 10 ga watan Agusta, 2018 yayin da za'ayi bikin a Landan a ranar 24 Satumba. 2018.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG