Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mesut Ozil Ya Ce Banbancin Launin Fata Ya Sa Shi Daina Taka Leda A Jamus


Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mesut Ozil, ya ajiye takalman buga wasa a kasar Jamus, yana mai bayyana cewa ana nuna masa banbancin launin fata tare da cin mutuncinsa.

Ana sukan dan wasan mai shekara 29 da haihuwa bayan ya dauki hoto da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya, a wani taro a Landon a watan Mayu.

Ozil, ya ce anyi ta tura masa da sakonnin cin mutunci da nuna kiyayya, sannan aka dora masa alhaki na rashin tabuka wani abun azo gani da Jamus batayi ba a gasar cin kofin duniya da ya gudana a Rasha.

Ya kara da cewar ni dan kasar Jamus ne a wurinsu a lokacin da muka yi nasara, amma ni dan cirani ne idan muka sha kashi," a wasa.

An haifi Ozil ne daga tsatson Turkawan da suka yi kaura zuwa kasar Jamus a garin Gelsenkirchen, kuma yana cikin tawagar ‘yan wasan kasar Jamus da suka lashe gasar kofin duniya a 2014.

Ya buga wa kasar wasannin sau 92 sannan sau biyar magoya baya na zabarsa a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kasar tun daga shekarar 2011, inda a bana tawagar kasar ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar kofin duniya 2018 a Rasha, duk da cewa suna daya daga cikin wadanda aka yi hasashen za su lashe kofin.

Dan wasan Mesut Ozil da Ilkay Gundogan na Manchester City dukkaninsu jamusawane 'yan asalin Turkiyya sun sha suka daga hukumar kwallon kafa ta Jamus bayan ganawarsu da Recep Tayyip Erdogan a watan Mayu.

A cikin wata sanarwa, da Ozil ya fitar ya ce, "ziyarar ba ta da alaka da siyasa. Kuma ni zuciya biyu nake da, daya a Jamus daya kuma a Turkiyya.

"Wannan ya sa ni wakiltar ofishi mafi girma a kasar iyaye na."

Ozil ya ce lokacin da yana karami, mahaifiyarsa ta gargadeshi da a kullum ya kasance mai girmamawa kuma kada ya taba manta asalinsa.

Ozil ya sake wallafa wani sako yana mai kalubalantar kafofin watsa labarai na kasar Jamus da suka dauki laifin rashin nasarar da kasar ta yi a gasar cin kofin duniya suka dora a kan hotunansa da shugaban Turkiya.

Dan wasan Ozil ya ce a ganawar da sukayi da shugaban kasar Turkiya sun tattauna ne game da kwallon kafa, sai jam'iyyar AK mai mulki a Turkiyya ta wallafa hotunan ana dab da zaben da Erodogan ya lashe.

Sanadin haka ‘yan siyasar kasar Jamus da dama sun soki Ozil da Gundugan, suna masu bayyana shakku kan amincinsu ga mutunta tsarin dimokuradiyar Jamus.

Jamus ta soki shugaba Erdogan kan yadda yake murkushe abokan hamayyar siyasa bayan murkushe wani yunkuri na yi ma sa juyin mulki. Sakamakon wanna lamarin na ritaya da maganganum da Ozil yayi

Hukumar kula da kwallon kafa ta Jamus (DFB) ta "yi watsi da zargin" wariyar launin fata daga da Mesut Ozil ya Fada amma tace ce zata iya duk abunda ya dace domin kare masa mutunci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG