Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Ta Dare Teburin La-liga 2016/2017 Mako Na 25


A cigaba da fafatawa da akeyi a kasar Spain bangaren La-liga na shekarar 2016/2017 mako na 25, jiya laraba 1/3/2017, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa Sporting Gijon da kwallaye 6-1.

Osasuna ta sha kashi a hannun Villarreal daci 4-1, Real Madri, ta yi canjaras 3-3 tsakaninta da Las Palmas, Granada ta doke Alaves da kwallo 2-1 Celta Vigo, na da 2 Espanyol nada 2.

A yau kuma za'a kara tsakanin Deportivo, da Atletico Madrid, da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya da Nijar.

Bayan kammala wasan na jiya Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta samu hayewa zuwa mataki na daya a saman teburin La-liga, da maki 57 a wasanni 25 da ta buga.

Ta sauke abokiyar hamayyarta Real Madrid, wadda ta dade akan matsayin Real Madrid, yanzu haka tana mataki na biyu ne a saman tebur da maki 56 a wasanni 24 da ta yi, Sevilla tana mataki na ukku da maki 52.

A Kasan tebur kuwa Granada, na mataki na goma sha takwas da maki 19, Sporting Gijon, tana mataki na goma sha tara da maki 17, Osasuna tana Kasan tebur a matsayi na ashirin da maki 10.

A kasar Ingila Manchester City ta samu nasarar zuwa zagayen na kusa da na kusa da na karshe (Quarter Final) a gasar cin kofin kalu bale (FA Cup 2016/2017) bayan da ta doke takwararta ta Huddersfield Town daci 5-1

A ranar Asabar 11/3/2017 zata gwabza tsakaninta da MiddleBrough da Manchester City, don nema zagaye na gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG