Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsene Wenger Ya Yi Watsi Da Tayin Fam Miliyan £30 A Shekara


A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya Chelsea, na zawarcin dan wasan gaba na Real Madrid, Alvaro Morata, da zarar an bude saye da sayarwar ‘yan wasa.

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus, dake kasar Italiya tace bata da niyar sayar da dan wasan gabanta mai suna Leonardo Bonucc,i Wanda Manchester city, da Chelsea, suka sama kudi yuro miliyan €60.

Inter Milan tana zawarcin James Rodriguez, daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Manchester City, ta ware yuro miliyan €60, domin sayen dan wasan Monaco, mai suna M'Bappe.

Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, yayi watsi da tayin da wata kungiya ta yi masa daga kasar Sin, na fam miliyan £60 a shekara.

Mai tsaron raga na kungiyar Chelsea, Courtois, yace har yanzu bawata tattaunawa da sukayi da kungiyarsa kan batun tsawaita kwantirakinsa a kungiyar.

Everton tana sha'awar kaftin na kungiyar Manchester united, Wayne Rooney, da ya dawo taka leda a kungiyar a karshen kakar wasan bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG