Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kece Raini A La-liga 2016/2017 Mako 25


A cigaba da gwabzawa da akeyi a bangaren La-liga na shekarar 2016/2017, mako na 25, a can kasar Spain jiya Kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad, tayi canjaras 2-2 tsakaninta da Eibar, Malaga tasha kashi a hannun Real Betis daci 2-1, Valencia ta doke Leganes da kwallo 1-0.

A yau kuma Barcelona, zata kara da Sporting Gijon, Osasuna da Villarreal, da misalin karfe bakwai da rabi na yamma agogon Najeriya da Nijar.

Sai Real Madrid ta karbi bakuncin Las Palmas, Granada da Alaves, Celta Vigo, zata gwabza da Espanyol, Su kuma da misalin karfe tara da rabi na dare agogon Najeriya, Nijar, da Kamaru da kasar Chadi.

A kasar Ingila kuwa za a sake kece raini ne tsakanin Manchester City, da Huddersfield town, a bangaren Cin kofin kalu bale FA Cup 2016/2017 zagaye na goma sha shida karawa ta biyu da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG