Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba’a Sanya Mu a Tallace Tallacen Kamfanoni Inji B Merry


Mawaki Abdullahi Isma'il B Merry
Mawaki Abdullahi Isma'il B Merry

A shirinmu na nishadi a yau mun sami bakuncin mawaki Abdullahi Ismail wanda aka fi sani da B Merry rapper wato mai wakar zaurance.

B Merry, ya ce ya fara harkar waka ne sakamakon yawan jin wakoki da ya ke yi tun yana dan yaro ,daga bisani ya fara bin masu mandiri inda yake taya su amshi da rike speaker da haka da haka har ya fara waka har kawo yau.

Ya ce yakan je yin MC inda yake cewa a sa mishi kide kide daga nan yake dora amshi ko zaurance har ya kawo, yanzu.

B Merry ya ce babban abinda yake ci masa tuwo a kwarya bai wuce yadda basa samun goyon baya ba daga wajen yan arewa mussamam ma a fanni tallatar da wakokin da sanya su a tallace tallace misali na kamfanonin salula kamar yadda ake yi wa mawakan kudu.

Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar da B Merry a Dandalinvoa.com

XS
SM
MD
LG