Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Mutane 9 a Kano Da Sabulu Na Jabu Na Naira Miliyan 11


'Yan Sanda a jihar Kano sun cafke wasu mutane 9, da ake zargi da sayarda sabulu na jabu.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Kano Magaji Majiya, ya tabbatar da labarin ga maneme labarai.

Ya ce an cafke mutanen ne a kasuwar Sabon gari biyo bayan korafe korafe da wasu ‘yan kasa na gari, rundunar ta yiwa mutanen kwanton bauna ne inda suka yi awon gaba da mutane 9.

Kakakin ‘yan Sandan ya ce an samu katan sabulun guda 1,301, wanda kudinsu ya kama Naira miliyan 11.1.

Ya ce da zaran an kamala bincike za’a gurfanar da mutane gaban kuliya, ya kuma umarci jama’a dasu ci gaba da baiwa jami’an ‘yan Sanda goyon baya.

XS
SM
MD
LG