Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashin Uba Ya Kashe Tagwayen Jarira, Kakan Su Da Kanshi


Jarirai
Jarirai

A karshen satin da ya gabata ne wani matashi mai suna Gawain Rushane, ya kashe tagwayen jarirai da budurwarshi ta haifa. A cewar hukumomi na karamar hukumar Jacksonville, a jihar Florida ta nan kasar Amurka. Mr. Gawain, ya shiga gidan da suke zaune yasa budurwar shi maman ‘yayan ta rike yaran jarira guda biyu a hannun ta, sannan yasa bindiga ya harbe ‘yayan biyu har lahira.

Daga baya kuma yasa bindiga ya harbe baban yarinyar shima har lahira, duk bayan haka sai shima ya saka bindigar a kanshi ya kashe kanshi. Yanzu haka dai maman yaran Megan Bateh, mai shekaru ashirin da biyu 22, tana asibiti kwance.

A lokacin da manema labarai suka zanta da mahaifiyar yarinyar, ta bayyana cewar, yarinyar ta gaya mata cewar yakashe yaran don ya nuna mata wasu daga cikin hallayyan shi. Tun bayan haihuwar tagwayen yaran ta lura da cewar yarinyar ta tana cikin wani hali, don haka yasa suka bukaci da ta dawo gida inda zasu dinga ganin ta da daya yarinyar ta. Har ya zuwa yanzu hukumomi na cigaba da bincike don gano dalilin da yasa matashin ya aiwatar da wannan danyen hukuncin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG