Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yi Batan Dabo Da Naira Miliyan 45 EFCC Na Nemansa


EFCC
EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC, na neman wani mutune mai suna Jerry Ogbonna Obike Phillip, ruwa a jallo.

Shi dai Ogbonna Phillip, ana neman sa ne saboda ya fidda wasu kudade da akayi kuskuren sawa a cikin ajiyarsa a banki.

Hukumar ta EFCC, a shafinta na Facebook, ta ce tana neman Ogbonna Phillip, a dalilin sata.

Phillip,wanda hukumar ta EFCC, ke nema ya yi batan dabo da wasu kudade har Naira miliyan 45, da aka yi kuskuren sasu cikin ajiyarsa a wani banki a Najeriya.

Ko kafin a farga a dai daita alamarin Phillip, ya jeye kudaden kuma ya cika wandon sa da iska.

XS
SM
MD
LG