Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Fuskantar Kalubale da Jami’an Otel- Otel -Inji Abdulaziz Small


Abdulaziz Small Kannywood
Abdulaziz Small Kannywood

A shirinmu na nishadi a yau mun sami zantawa da wani jigo a harkar fina finai a Kannywood, Abdulaziz Ahmad Small mai shirya fina-finai a yanzu.

Abdulaziz Small ya ce ya shiga harkar fim sanadiyyar yadda mutane ke yi wa yan fim kallo, hakan ne ma ya sa ya tsunduma harkar domin canza tunanin mutane a kan hakan.

Small ya ce ya fara harkar fim ne tun daga tushe ya fara da dan aiki , daga bisani ya zama mai raba kaya har kawo yanzu ya zama mai shiryawa.

Abdulaziz Small dai ya shafe shekaru 20 yana fim, ko da yake ya ce babban kalubalen da ya ke fuskanta a wannan harka bai wuce yadda idan sun je daukar fim a wani otel masu otel kan yi musu wani kallon da bai dace ba da sunan sune bata gari kuma aikin ma da su ke yi na bata tarbiyar yara.

A fannin tsegumi kuwa daukacin masu ruwa da tsaki da wakilan gwamnati suka hadu domin tattauna da samawa masanaartar alkibila.

XS
SM
MD
LG