Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawaitar Tsofaffin Na'urorin Zamani Na Shafar Yanayi Da Tattalin Arzikin Duniya


Wani sabon rahoto ya gano matsananciyar barazana ga muhalli da lalatattun kayan na'urarorin zamani ke haifarwa, kamar wasu bangarori na wayar hannu, talabijin, kwamfuta, kakuleta, da dai makamantan su.

Matsalar tana shafar lafiyar mutane da tattalin arzikin kasashe da dama a fadin duniya. Wakiliyar VOA Lisa Schlein, ta hada wannan rahoton a wani taron kasa-da-kasa na kungiyoyin sadarwa na duniya a birnin Geneva.

Kungiyar manema labarai ta duniya, na aiki gabanin kungiyoyin sadarwa na kasa-da-kasa, inda suka bayyana cewar, kimanin rabin mutane a duniya suna amfani da daya daga cikin na’urorin zamani.

Ko dai wayar salula, kwamfutar hannu, talabijin, firij, da ma sauran na’urori kirkirar nasara, duk a cewar masana binciken tsofaffin na’urorin, Mai magana a madadin su Mrs. Vanessa Gray, ta bayyana cewar karin yawaitar na’urorin zamani a duniya ya taimaka matuka wajen yawaitar lalatattun na’urorin zamani.

A shekarar 2016 kawai an samu lalatattun na’urori da nauyin su ya kai metrik milliyan 44.7, wadanda kawai aka zubar a shara. Gray, ta kara da cewar duk wata na’ura da ake cajin ta, ko take aiki da batiri wanda suka lalace suna da illa ga yanayi da lafiyar bil’adama.

Rahoton ya bayana cewar, kasashen yankin Asiya, ne suka samu kaso mafi yawa na lalatattun na’urori, sai kasashen Turai, kana kasar Amurka da wasu kasashen nahiyar Afrika.

Idan za’a maida kudaden da aka kashe wajen sayen wadannan lalatattun kaya na shekarar 2016 kadai, an kiyasta kudin su zai kai dallar Amurka billiyan hamsin da biyar $55B, wanda yawan kudin ya wuce tattalin arzikin wasu kasashe da dama a duniya.

Rahoton yana kara kira da a samar da dokoki da zasu ayyana yadda, za’a rika sarrafa tsofaffin na’urori, wasu kasashe a duniya sun aminta da sabon tsarin, kasancewar kashi 66% na yawan mutane a duniya sun fito ne daga kasashe 67, wanda suka aminta da dokokin tsarin zubar da lalatattun na’urori.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG