Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Gwamnatin Tarayya Na Koyawa Masu Yiwa Kasa Hidima Sana'oi Ya Fara Aiki


Matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) a jihar Gome sun yaba da sabon shirinnan na gwamnatin tarayya wanda ke koyawa masu yiwa kasa hidima sana’oin hannu da aka yiwa lakabi da Skills Acquisition Developemnet Programme ko (SAED) a takaice.

Da take zantawa da matasan, Mujallar Daily Trust, ta wallafa cewa daya daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin mai suna Miss Obarakpo, ta baiyana cewa yanzu ta iya yin takalman fata, kuma ta kara da cewa ta koyi yadda ake kera takalma da jakar hannu ta mata nau’uka daban daban a yayin da ake horas da su.

A cewar ta, kafin ta fara yiwa kasa hidima bata iya harhada irin wadannan kaya ba, amma yanzu kama daga jakar hannu ta mata zuwa takalma babu wanda bata iya hadawa da kanta ba.

Matasa da dama sun bayyana farin cikin su na samun wannan dama ta koyon sana’ar hannu, lamarin da wasu da dama ke ganin zai taimaka wajan dogaro da kai.

Sana’oin da matasan suka koya sun hada da sarfa nau’ukan abinci daban daban da lemun kwalba da saka jakar mata da takalma da harkokin gini da sauransu.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG