Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Inganta Mutunmutumi Da Ake Kirkira Don Magance Kutse


Taron masana kere-keren mutunmutumi ‘Robot’ da suka lashe yawancin kyaututuka, na masu kirkirar mutun mutumi mai hazaka sun fitar da wani sakamakon binciken su. Wanda yake nuni da cewar akwai rina a kaba, akan yadda ake inganta mutunmutumin da ake kirkira.

Sun bayyanar da cewar mafi akasarin mutunmutumin da ake kirkira, ba’a la'akari da wasu abubuwa da ka iya kai komo, a yadda mutunmutumin ke gudanar da ayyukan su. Kimanin kaso hamsin na mutun mutumin da ake kirkira, na iya zama babbar matsala ga masu amfani dasu a gidajen su. Domin kuwa suna iya cutar da mutane a wasu yanayin.

A cewar masanan, Mr. Cesar Cerrudo, da Mr. Lucas Apa, ‘yan kutsen sirri kan iya amfani da mutunmutumi wajen satar bayanan mutane ko leken asiri, wanda suke ganin yanada kyau a fito da wata ingantacciyar hanya, da za’a dakile amfani da robot wajen satar bayanan sirri.

Mutane da yawa kanyi amfani da mutunmutumi da ake amfani dasu a gidaje, wanda yakan rike wasu sirrikan mutane, wani lokaci har bayanan da suka shafi bankin mutun, da wurare da mutun ya kanje a wasu lokutta.

Ya zuwa yanzu masu kirkrirar mutunmutumi basu maida hankali, wajen inganta bangaren satar bayanai a jikin mutunmutumin ba, duk dai da cewar har a yau basu fara kutse ta amfani da mutunmutumin ba.

Amma akwai bukatar magance matsalar tun kamin sun maida hankali wajen. Sun kuma gabatar da wata takarda ga taron masana, wanda kimanin mutane 100 suka rattafama hannu da rokon majalisar dinkin duniya, ta hana kirkirar mutunmutumi dake kama da soja mai kisa, ko wasu makamai.

Suna ganin hakan zai kara harzuka fada da sha’awar kashe kashe a tsakanin yara da matasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG