Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alexis Sanchez Ba Zai Buga Wasan Arsenal Da Manchester United Ba


Tana iya kasancewa dan wasan Gaba na Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ba zai samu damar fafatawa a babban wasan da kungiyarsa zata yi da takwararta ta Manchester United ba a gasar firimiya lig ta bana mako na goma sha biyu, da za a buga a ranar tara ga watan Nuwamba na shekarar 2016.

Wannan ya kasance ne a sakamakon raunin da ya samu a wajan motsa jiki da kungiyar kwallon kafa ta kasarsa a shirye shiryen ta na gwabzawa da zatayi da kasar Chile a gasar neman shiga cin kofin duniya.

Ana hasashen Alexis Sanchez zai tafi jinyar sati shida sai dai wata majiyar na cewa ana ganin zai iya samun sauki kafin wannan ranar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG