Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yemi Osinbajo Yace Za'a Baiwa Super Eagles Isassun Kudade


 Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, zata fafata da takwararta ta Algeria, a ci gaba da neman gurbin a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, wanda zai gudana a kasar Rasha. Tun farko dai Najeriya, ta doke kasar Zambia, a fafatawar da suka yi a kasar Zambia.

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yiwa ‘yan kungiyar ta Super Eagles, alkawarin cewa Gwamnati zata tabbatar da gani cewa an samar masu kudade da duk aninda suke bukata domin martaba Najeriya.

Mataimakin shugaban ya furta haka ne a lokacin da ya ziyarci ‘yan kungiyar a filin wasa na Abuja, gabanin wasan su da kasar Algeria.

Yace samun nasara akan Algeria, yana da mahimmaci ga Najeriya, kuma ya kara da cewa yana da kafin guiwar cewa Najeriya, zata yi rawar ganin da zai bai duniya mamaki.

Farfesa Osinbajo, yace doke kasar kasar Zambia, da najeriya, tayi wani manuniya ce cewa kasar ta doshi hanyar zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.

XS
SM
MD
LG