Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Mata Da Suka Fi Karfin Maza


Biyo bayan sakamakon zaben Amurka, wanda ya nuna cewa Donald Trump, wanda ya tsaya takara a inuwar jam’iyyar Republican, ya lashe zaben, mata a tarayyar Najeriya, sun nuna juyayin rashin samun nasarar Hillary Clinton, wanda ya kawo cikas ga fatan mace ta farko da zata shugabaci Amurka.

Matan dai na ganin cewa da Hillary, ta samu nasara da hakan ya kara budawa mata hanyar ci gaba a fafutukar da suke yi a fadin duniya.

Kama daga kan Ellen Johnson, shugaban Liberia, da tsohuwar shugaban Malawi Joyce Banda, mata na ganin cewa hakarsu ta taka rawa a manyan madafun iko zasu tabbata da takarar ta Hillary Clinton, ganin cewa kasashen Inhila da Jamus duk mata ke shugabanci.

Abubakar Sadiq, dake sharhin kan siyasa, na murnar nasarar da Trump,ya samu amma yana mai cewa ya kamata a sake mata suyi abinda yakamata, yana mai cewa akwai mata da dama da suka fi karfin masa.

Face an ga kamun ludayin Trump, a kwanakin dari akan mulki ba za’a tabbatr da kalamansa ba kurari ne ko kuwa lalle da gaske yake yi ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG