Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Karamar Hukumar Kasada


Wasu ‘yan bindiga, sun kai hari karamar hukumar Kasada, dake cikin jihar Katsina, harin da yayi sanadiyar mutuwar mutun daya Na’ibin Limamin Kasada, Malam Badamasi Abdullahi da raunata wasu da dama.

Wani wanda akayi abin akan idonsa yace ‘yan bindiga sun farwa gidaje a unguwanin Makera, Marina, Yara-Gabas, Yara-Arewa da kofar-Fada.

Yana mai cewa sun datse hanyoyin zuwa wadannan wurare suka dingi harbi na razana mutane domin su samu damar ci gaba da mugun aikin da sukeyi.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar DSP Salisu Agaisa, wanda ya tabbatrr da labarin yace sun cafke mutun daya kuma sun dukufa neman sauran.

XS
SM
MD
LG