Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Ya Tabbatar Da, Yawan Karance-Karance Na Kara Lafiyar Kwakwalwa!


Littattafai
Littattafai

Karance-karance abune da aka sani a matsayin abu mai matukar mahimanci ga rayuwar dan’adam, musamman wajen samun kwakwalwa mai nagarta, a lokacin kuruciya. Wasu bincike da dama da aka gabatar da suka bayyanar, da karin alfanu ga yawan karance-karance.

Yawaita karance-karance na kara ma mutane tsawon rayuwa mai amfani, duk mutumin da ya dauki karatu a matsayin dabi’ar yi a rayuwar yau da kullun, zai kasance mai bama kwakwalwar shi abincin da take bukata don girma.

Mujallar binciken rayuwar dan’adam da magunguna, ta jami’ar Yale, dake kasar Amurka, ta tabbatar da cewar babu rabin abun da mutun ya karanta, wanda bai zai amfanar dashi ba. Abu mai matukar mahimanci a nan shine, mutun yayi karatu, koda kuwa wane irin ne, amma ya zamana karatu ne da zai amfanar da rayuwar mutun.

Sun cinma matsaya bayan wani bincike da suka gudanar akan wasu mutane 3,635 wanda suka raba su gida biyu, rabin mutanen sun karanta kasitu da jaridu na tsawon sati biyu, su kuwa sauran basu karanta komai ba, a karshe binciken ya bayyanar da mutane da sukayi karatu sun fi lafiya, walwala da annashuwa.

A takaice binciken na nuni da irin mahimancin dake tattare da karatu kowane irin ne ga matasa, don samun ilimi kana da samun lafiya mai inganci a tsawon rayuwar su, har zuwa lokacin tsufa. Karatu ya bayyana a matsayin abu da ya kamata kowa ya saka a cikin tsarin shina yau da kullun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG