Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Gidan Kashe Ahu! Abincin Wani Gubar Wani!


Taswirar Duniya
Taswirar Duniya

Wasu dabi’u da a wasu kasashe ba wani abu bane, amma a wasu kasashen idan mutun yayi su zasu jefa shi cikin fitina. A kasar Austrlia, karya doka ne mutun ya manna wani hoto, ko yin rubutu a jikin wani gini, ko dai na wani mutun ko na gwamnati. Yin hakan zai sa a yanka ma mutun tara da zata kai $380 wanda tayi dai-dai da naira dubu dari da hamsin, ko gidan wakafi.

A kasar Singapore, babban laifi ne mutun ya dinga amfani da damar yanar gizon makoci “Wi-Fi” idan kuwa aka samu mutun da wannan aika-aikan, za’a yanka mishi tara da takai $10,000 dai-dai naira milliyan hudu, ko kuwa mutun yaje gidan yari na wasu shekaru.

Hakama a kasar Birtaniya, idan mutun ya saka na’urar bayyana barawo kodai na gida ko na mota, da zai dinga kara batare da kaukautawa ba, hakan zai sa a yanke ma mutun tara, da tana iya kaiwa $6,500 kimanin naira milliyan biyu da dubu dari biyar.

A kasar Amurka kuwa karya doka ne a samu mutun ya saukar da wandon shi kasa wanda hakan zai bayyanar da wani bangare na jikin shi, hakan zai sa a yanke ma mutun tara na $1,000 wanda tarar na iya kaiwa naira dubu dari hudu, ko kuma mutun yaje gidan yari na wasu watanni.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG