Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa A Kama Sana'a Domin Ragewa Iyaye Dawainiya


An bukaci matasa mussamam mata da su zamo masu sana'ar hannu domin dogaro da kai, ko da kuwa suna makarantun gaba da sakandare.

Matashiya Fatima Yusuf Jibrin ce ta bayyana haka a yayin tataunawa da DandalinVOA , ta ce a yazu haka ta kammala makarantar ta, ta sakandare kuma bata samu damar shiga jami'a ba.

Ta dalilin haka ne matashiyar ta kama sana'ar kwaliya ga amare da mata masu bukata kafin lokacin da zata samu shiga jami'a.

Fatima ta kara da cewa baya ga kwaliya tana saka, ta abin da mata ke amfani da shi wajan kama gashi, domin a cewar ta, tana bukatar tsayawa da kafarta kuma koda ta samu shiga jami'a zata ci gaba da sana'arta domin ta rage wa iyayenta dawainiya.

Saurari hirar a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG