Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Ruwan Soyayya Da Tsufa, Wani Matashi Ya Auri Sirikar Shi!


Aure a kasar India
Aure a kasar India

Suraj Mahto, mai shekaru 22, da haihuwa, ya shiga cikin jerin mutane da suka kafa tarihi a fadin duniya. Inda ya bar matar shi maman ‘dan shi, Lalita, ya auri mahaifiyar ta, Asha Devi, mai shekaru 42.

A kasar India, an samu wani matashi, yana auren wata yarinya, ta kamu da rashin lafiya, wanda hakan yasa ya maida ta gidan su, a lokacin da take jinya, ya kanje gidan don duba lafiyar ta, daga nan sai ya shiga lambun soyayya da mahaifiyar yarinya.

Sun kwashe tsawon shekara suna soyayya, wanda a watan Yuli, na wannan shekarar su kayi aure. Ya rabu da matar ta shi ya auri sirikar shi. Watanni kadan da yin auren su, ya bayyanar da cewar lallai yayi kuskure, na auren sirikar shi.

Ya roki matar tashi da ta gafarta mishi, kuma ba zai sake daukar sirikar tashi a matsayin matar shi ba. Daga yau yana bukatar koma, matar shi ita kuma sitikar shi ta zauna a matsayin ta na sirika. Baki daya jama’ar garin Puraini, a jihar Bihar ta kasar India, sun nuna rashin yardar su da wannan auren, don ya sabama koyarwar al’adun su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG