Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimiyya Da Fasaha: Karni Na 21 Karni Na Dakilewar Kwakwalwa!


Kimiyya Da Fasaha
Kimiyya Da Fasaha

Karni na ashirin da daya “21st Century” a turance ya maida mutanen wannan zamanin wasu malalata. Da yawa yanzu za’a ga yadda danganta ke kara tabarbarewa, a sanadiyar cigaba da aka samu na kimiyya da fasaha. A wani bangaren kuma za’a ga irin cigaba da aka samu, musamman ta yadda mutane kan sada zumunci a sauran sassa na duniya.

Mutane da dama na nuna rashin jin dadin su, da yadda abubuwan kimiyyar zamani suke sa mutane ke barin al’adun su, ko wasu abubuwa da suke da matukar muhimanci a rayuwar su, misalin yadda mutane basa amfani da kwakwalwar su wajen haddace abubuwa, ko karatu da zai amfani rayuwa.

Duk a sanadiyar mutane kan iya amfani da wayoyin hannun su, kwamfutocin zamani, da duk wasu abubuwa masu kama da hakan. Wasu kuwa suna ganin ai wannan wani cigaba ne, da zai kai duniya wani mataki. Hasali ma, suna ganin kamar wadannan kayan zamanin ne suka sa duniya ta kai inda take a yanzu.

Masana sun tabbatar da cewar, babu shakka idan mutane suka duba irin halin da ake ciki, hali ne na cigaba wanda yake bukatar mutane a wannan zamanin, suyi amfani da damar wajen kara amfani da kwakwalwar su, don magance wasu abubuwa da kan iya zama damuwa a nan gaba. Kuma suyi amfani da wadannan kayan zamanin don kara tunanin ya gobe zata kasance.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG