Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Suma Mutane Ne Masu Tarbiya Kamar Kowa


Lawal Ahmad

A yau bakunci fitattacen jarumin nan Lawal Ahmad muka samu wanda ya shafe shekaru yana sana'ar fina-finai ya ce abinda ya fi ci masa tuwo a kwarya bai wuce yadda alumma ke yi wa masu harkar fim kallon da bai da ce ba.

Yana mai cewa babban makiyan masu harkar fina finai basu wuce wadanda basu fahimci mahimmancin masana’antar ba, da irin gudumarwar da masana’antar ke taimakawa dashi wurin ilimantar da jama’a da samarwa matasa aiyukan yi.

Ya ce ya kamata mutane su san cewar fim sana'a ce ba dabi'un masu wannan sana'a ba, kuma ya kyautu jama’a su san cewa masu wasannan sana’ar mutane ne masu tarbiya kamar kowa.

Lawal ya kara da cewa yanzu ya fara sana'ar fina-finai kuma burinsa ya kai kololuwar bisa a harkar fina-finai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00

XS
SM
MD
LG