Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Frank Lampard Na Son Zama A City In Ji Pellegrini


Manajan Manchester City, Manuel Pellegrini.
Manajan Manchester City, Manuel Pellegrini.

Manajan Manchester City, Manuel Pellegrini, yace Frank Lampard ya bayyana aniyar zama a kulob din har zuwa bayan wa’adin hayarsa daga kungiyar kwallon kafa ta New York City FC ta nan Amurka.

A watan Yuli ne Lampard ya yarda zai koma New York City FC wadda ke kawance da kulob din ta Firimiya Lig, amma tun daga lokacin har zuwa yanzu yana ci gaba da wasa a Manchester City ganin cewa kakar kwallo ta MLS a nan Amurka ba zata far aba sai a watan Maris.

Koda yake an shirya zai zauna zuwa karshen watan nan na Disamba ne, Lampard ya nuna cewa har yanzu da sauransa, inda ya jefa kwallaye 6 a wasanni 14 da ya buga. Sergio Aguero ne kawai ya fi shi jefa kwallo ma Manchester City a wannan kakar kwallon.

A halin da ake ciki, manajan daya kungiyar ta Manchester, watau Uni8ted, Louis Van Gaal, yace Robin van Persie ya amsa kiran da yayi masa ta hanyar sukar yadda yake wasa a bayan doke Arsenal da United ta yi da ci 2-1 a watan da ya shige.

Dan wasan dan kasar Netherlands ya amsa wannan suka ta hanyar da ya sani, watau ta hanyar zura kwallaye cikin raga, inda ya watsa guda uku cikin wasanni ukun da suka shige.

XS
SM
MD
LG