Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koch Brendan Rodgers na Liverpool Yace Shine ya Cancanci Zama Koch din Liverpool


 Liverpool.
Liverpool.

Koch din Liverpool Brendan Rodgers, yace shine ya cancanci, zama Koch din kungiyar, ta Liverpool, duk da dan koma bayan da aka samu, a kakar kwallon bana.

Kwollayen da Luis Suarez, da Daniel Sturridge, suka jefa a raga, a kakar wasan, a bara ya taimakawa, kungiyar, inda ta zo kusa da cin kofin Primiya Lig, inda Manchester City, ta wuce ta da maki biyu, kachal.

Gashi Suarez, yanzu ya koma kungiyar Barcelona, kuma Sturridge, yana jinyar raunin da ya samu .

A yanzu Liverpool, ne, ta tara a teburin Lig, din, kuma zata kara da kungiyar Manchester United, ranar lahadi. Koda yake Liverpool din tayi kunnen doki da Basel a tsakiya mako.

Rodgers, yace “sako na shine cewar bana tsammanin akwai wanda yafi ni cancantan zama Koch din Liverpool,” ya kara da cewa watani bakwai da suka wuce kungiyar ta Liverpool ta zo kusa da cinye gasar.

liverpool - 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

XS
SM
MD
LG