Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Raul Ya Koma New York Cosmos, Amma Ba Don Buga Kwallo Kawai Ba


Raul Gonzalez, shahararren dan wasan kwallon kafa ne dan kasar Spain, wanda duk wani mai sha’awar kwallo ya san shi domin yayi abubuwan tarihin da a zamaninsa babu wanda yayi musamman a kungiyar Real Madrid, kafin ya tafi Schalke.

A yanzu Raul mai shekaru 37, wanda ke dab da shiga matsayin da watakila ba zai iya buga kwallo ba, ya samu wani abin kuma wanda yace ya fi masa jefa kwallo a cikin raga. Ba wai ya daina wasan ba ne kwata-kwata, domin ya rattaba hannu kan kwantaraki da kungiyar kwallon kafa ta Cosmos ta New York a nan Amurka a kan zai buga mata. Sai dai kuma, babban dalilinsa na yin hakan, shi ne zai samu damar zamowa darektan makarantar koyar da wasan kwallo ta yara da matasa ta kungiyar, abinda yace dalilinsa na zuwa daular Qatar ke nan shekarun baya.

Raul yace wannan yana da muhimmanci a wurinsa, domin babu abinda ya fi burge shi kamar ya koyar da wassan kwallon kafa ga matasa, ya ga wanda ya koyar shi ma ya zamo wani abu a fagen kwallo a duniya. Yace yana kuma da muhimmanci a koyawa yaro yadda ya kamata ya doshi buga kwallo tun bai girma ba, domin ya tashi da shi a jikinsa.

Raul yace wannan aiki ne da zai dauki shekara da shekaru, ba wai na shekara day aba, don haka, ya zo da niyyar zama a NYC na lokaci mai tsawo.

XS
SM
MD
LG