Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallon Kafar Almeria ta Tsallake Rijiya da Baya


 Kungiyar Kwallon Kafa ta Almeria
Kungiyar Kwallon Kafa ta Almeria

Kungiyar kwallon kafar Almeria, ta kasar Spain, tayi ban kwana da Koch din ta Francisco Rodriguez, biyo bayan sha kashin da kungiyar tayi so takwas a jere.

Wannan sakamakon na rashin tabuka abun arziki, na kungiyar kwallon kafar na Almeria, ya jawowa Koch din rasa aikin sa.

Dan shekaru 36, Rodriguez, ya kasance Koch din Almeria, tun kakar kwallon bara, korar sa, yazo ne kwana daya bayan da kungiyar ta kwashi, kashinta, a hannu inda kungiyar Eibar, ta nakadamata kashi, da ci biyar da biyu .

Kungiyar Almeria, dai itace ta uku daga kasan teburin lig, inda ta tsallake rijiya da baya na kumawa matakin na kasa.

Almeria, ta kasa cin koda wasa daya a gida a kakar wasa na bana, Rodriguez, shine na 4 a jerin Koch din da aka sallama a manyan kungiyoyi ashirin.

Koch Rodriguez - 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

XS
SM
MD
LG