Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan Sana'oi Abin Dogaro


Zainab Dahiru
Zainab Dahiru

A shirin mu na kananan sana’oi a yau DandalinVOA ya samu bakuncin Zainab Dahiru- uwa mai yaya tara ta ce ta fara sana’a ne domin ta zama ta magance dukkanin bukatun da ke gabatan mussamam ma kasancewar mahaifin yaran ya dade da rasuwa.

Ta kara da cewa ta fara da sana’a jaka ‘yar karama wacce ta ke kai wa kofar Wambai inda suke sara, daga bisani ta fara kwaikwayan jakuna zamani ba karama ta hannu ba shina ta ke kai wa kasuwa.

Zainab ta ce daga yin jaka sai ta kuma koyi yadda ake in Tumtun , da carpet na tsakiyar daki da ‘yan kananan pilo wanda ake kawata daki da su da kuma irin wadanda ake sawa akan kujeru.

Ta ce ‘yayanta mata biyu na taimaka mata wajan wannan sana’a na ta inda ta ke cewa tana kuma yin kayan jarirai da katifar kwanciya da kuma abinda ake saka kayansu jarirai idan za’a je unguwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG