Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangal Fim Din Aamir Khan Ya Samarda Kusan Dala Milyan $300


Aamir Khan
Aamir Khan

Fim din Dangal na shahararren jarumin Bollywood din nan Aamir Khan, ya samarda tsabar kudi kusan dalar Amurka miliyan dari uku, ($300), kuma ya kasance fim din da yafi kasuwa a kasar China.

Wannan nasarar da fim din ya samu kashi biyu cikin kashi uku na adadin kudaden da fim din ya samar an samesu ne a kasar China, mutanen kasar ta China dai na matukar son fin din Dangal, kuma kusan basu gajiya da kallonsa.

Aamir Khan, dai na da dimbin masoya a kasar China, kamar yadda mafi yawan su ke kiransa “Uncle Khan” kasansewarsa jarumin da suka fi kauna a cikin jaruman kasar Indiya, fina finan Aamir Khan kamar 3 Idiots da PK kafin fitowar Dangal, suma sun taka rawar gani a kasar ta China.
Koda yake an yi harsashen cewa fim din Dangal zai samarda dalar Amurka, miliyan dari uku da ashirin ($320) amma wannan fim din zai dade a zukatan matasan China.

Wannan fim din da jarumi Aamir Khan, yi ya kasance wanda ya fi tashe kuma da kasuwa a China wanda kuma ba daga Hollywood, ya fito ba.

Shi dai wannan fim din tarihin wani dan kokawa ne wanda daga bisani ya koyawa ‘ya’yansa mata kokawa ta yadda zasu shahara a duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG