Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zama Daram A Real Madrid ! Cristiano Ronaldo


Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kammala sayen tsohon dan wasantan kuma kaftin a kungiyar kwallon ta Manchester United Wayne Rooney, wanda ya bar kungiyar ta Everton zuwa Manchester a shekara 2004 kimanin shekaru 13 da suka wuce akan kudi fam miliyan £25.6 a lokacin inda a yanzu Everton ta sayeshi akan fam miliyan £10.

Kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniyar ne bisa musanya tsakanin ‘yan wasan su Romelu Lukako da Wayne Rooney inda ita kungiyar ta Manchester United, zata yiwa Everton cikon kudi yadda ta saye Romelu Lukako har fam miliyan £75.

Rooney dai ya buga wasanni sau 559 wa kungiyar Manchester united inda ya Zurara kwallaye guda 259.

Everton tace zata ba Rooney riga mai lamba Goma wacce Lukaku ke sawa lokacin da yake kungiyar ta Everton.

Shima shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya mai taka leda a kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo ya amince zai ci gaba da zama a kungiyarsa ta Real Madrid ta kasar Spain.

A kwanan bayane dan wasan ya nuna sha'awarsa na barin kungiyar ta Real Madrid sakamakon fushi da yayi na tuhumarsa da hukumomin kasar Spain sukayi na rashin biyan harajin da ya kai har fam miliyan £14

Wanda dan wasan ya musanta.

Sai dai ranar 3, ga watan Yuli 2017 dan wasan zai baiyana a gaban kotu don kare kansa daga wannan zargi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:39 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG