Zauran matasa na yau an tattauna ne kan bukatun matasa ga gwamnati mai jiran gado da Madina Dauda ta jagoranta a babban birnin tarayya Abuja.
Bukatun matasa ga shugaba mai jiran gado, abu na farko shine a baiwa matasa dama domin su bayar da gudunmawar su a harkar siyasa, ya kamata a baiwa matsa dama wajen karatu domin samin ilimi mai nagarta, sai kuma aikin yi ga matasa kasancewar yawancin matasa na da karatu amma babu ayyukan yi.
A ganin ‘daya daga cikin masu tattaunawar na ganin kalubalen da yake tattare da matasan Najeriya shine matasan basu san ciwon kansu ba, kira ga gwamnati kuwa shine ta tabbatar da cewa ta baiwa matasan damar samun ilimi, kasancewar ilimi shine hasken duniya samun ilimi na kowanne irine shine zai taimakawa matasa wajen samun aikin yi da dogaro da kai.
Taibiyyar matasa babbar matsala ce a halin yanzu idan aka duba yadda matashi wanda ke da ilimi amma babu tarbiya mai kyau, wanda hakan na taimakawa wajen hana shi samun aiki, aiki kan gina da gyara tarbiya wata hanyace da zata tabbatar da cigaba ga matasa da kasa baki ‘daya.
Saurari cikakkiyar tattaunawar Zauren Matasa.