Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Da Gwamnati Mai Jiran Gado Zata Fuskanta


An unidentified woman sells Nigerian national flags, during an event to mark Nigeria independence day, in Lagos, Nigeria. Tuesday, Oct. 1, 2013 . Nigeria marked 53 years of independence Tuesday with little to celebrate, scores of families are in mourning
An unidentified woman sells Nigerian national flags, during an event to mark Nigeria independence day, in Lagos, Nigeria. Tuesday, Oct. 1, 2013 . Nigeria marked 53 years of independence Tuesday with little to celebrate, scores of families are in mourning

Gwamnati mai jiran gado na da tilin ‘kalubale a gaban ta da suka hada da cin hanci, rashawa, da ‘dinbin bashin makurden kudade da ake bin Najeriya, kan yadda gwamnati zata iya samun kudaden da take bukata wajen yin ayyukan da suke gabanta, munji ta bakin Dakta Mustapha Muktar na sashen nazarin tattalin arziki a jami’ar Bayero.

Wanda ke ganin wannan sabuwar gwamnati da zata karbi mulki ranar ashirin da tara ga watan mayu na wannan shekara ta 2015, zata sami kalubale na basussuka da gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya suka ci, bashin dai ya rabu kashi biyu na farko akwai bashin cikin gida, akwai bashi na waje, bashin cikin gida dai shine bashin da gwamnati take ci daga kamfanoni da masu yin hada hada, bashin waje kuma shine bashin da gwamnati take ci daga waje wanda shine bashin da yafi matsala ga kasa, domin duk lokacin da kasa bata biya wannan bashi ba to mutanen dama ba’a haifesu ba zasu zo su gaje shi kuma dole ne su biya.

Dakta Mustapha na ganin gwamnati zata iya amfani da kudaden da za’a samo daga cin hanci da rashawa wajen rage bashin da ake bin Najeriya. Gwamnati na ciyo wadannan basussuka alokacin da ta gaza aiwatar da kasafin kudin ta, kasancewar Najeriya ta dogara ne ga man fetur, duk lokacin da farashin man fetur ya fadi wanwar a duniya wani lokaci gwamnati na rasa kudin da zata aiwatar da wasu ayyukanta batare da taci bashin wata kasa ba.

Hanyoyin da gwamnati mai zuwa zata bi sune, idan har aka bincika aka samo kudade da jama’a da ma’aikatu suka dawo dasu, ayi amfani da kudaden wajen biyan basussukan wajen biyan kudin ruwa da rage nauyin bashi, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa, hakan shine zai bayar da damar yin amfani da kudin kasafin wannan shekara wajen kawo ayyukan yi, samar da tsaro, kiwon lafiya, gyara tituna da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG