Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa Kan Auren Fiye Da Mace ‘Daya


Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013
Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013

A cikin Zauran matasa wakilin mu Ibrahim Abdulaziz dake Yola jihar Adamawa, ya tattauna da wasu matasa kuma ma’aurata kan batun yadda wasu mazaje ke auren fiye da mace ‘daya, wasu kuma suna auren mata ‘daya.

Tambayar dai a wannan zaure shine meyasa wasu maza ke auren fiye da mace ‘daya? Amsar ‘daya daga cikin bakin na zauren matasa shine; dalili na farko shine addinin musulunci ya nunawa namiji cewar zai iya auren mace fiye daya har zuwa hudu, saboda wannan dama da Allah ya baiwa maza, wasu na amfani da ita domin cika umarnin addinin musulinci. Haka kuma akwai lalura irin ta zama wadda idan mutum nada mata biyu alal missali, idan ‘daya bata nan tayi tafiya to a kwai mace a gidan da zata cigaba da gudanar da ayyuka da ‘dawarniyar gida.

Zama da mace fiye da ‘daya ta fuskar addini akwai umarni, umarni na wajibi da umarni wanda yake bana wajibi ba, inji daya daga cikin masu tattaunawar inda ya cigaba da cewa, zabi aka baiwa namiji ya auri mace ‘daya, biyu, ko uku ko hudu, amma akwai sharadi na auren, dayawa mutane na yin auren koda kuwa basu cika sharudda da ka’idojin auren ba.

Adalci shine ginshikin aure ga duk ma’aurata koda kuwa mutum ya auri mace ‘daya ko hudu, adalcin kuma bai tsaya kan mace kadai ba ya shafi yaya da zuriya baki ‘daya, domin ubangiji yana gargadin cewa, “in bazakayi adalci ba”.

Saurari cikakkiyar tattaunawar.

XS
SM
MD
LG