Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kano Pillars Ta Samu Nasara Kan Enyimba


Kungiyar ‘yan wasan Kano Pillars ta cigaba da kare gidan ta bayan da ta lashe wasan ta da zakarun Afirka, wato kungiyar Enyimba ta Aba daci 1 – 0 a filin wasan Sani Abacha dake Kano.

A cikin wasanin da ake na mako hudu, kungiyar Heartland ta Owerri ta lashe wasan da suka kara da kungiyar Kwara United a Illorin 3 – 1, haka kuma kungiyar Wikki Tourists ta lashe nata wasan 2 – 1 a can gidan Abia Warriors.

Kungiyar Lobi Stars ta sami sa’ar samun maki a gidanta, bayan da ta dawo baya lokacin da tayi kunnen doki da kungiyar Sharks ta Port Harcourt, bayan haka dai kungiyar Shooting Star ta samu damar yin kunnen doki da Nasarawa United a wasan da akayi a can Lafia.

Enugu Rangers dai sun sha kashi a gidan su 1 – 0 daga bakin su Giwa FC ta Jos. Daga karshe kungiyar Prince Aggrey ta samu nasarar lashe wasanta a lokacin da aka tafi wasan karin lokaci, wanda hakan ya taimakawa kungiyar Sunshine Stars da maki uku kan abokiyar hamayyarta ta Dolphines a Akure.

XS
SM
MD
LG