Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Dan Iya Kan Rawar Da Mata Zasu Iya Takawa


Kwararru da suka kunshi Dr. Ibrahim O. Salau, Emmanuel Ogebe, da Sandra Ekpenyong na shirin yin fashin baki akan muhimmancin ilimin yara mata da satar daliban Chibok.
Kwararru da suka kunshi Dr. Ibrahim O. Salau, Emmanuel Ogebe, da Sandra Ekpenyong na shirin yin fashin baki akan muhimmancin ilimin yara mata da satar daliban Chibok.

Da yake ‘Dan Iya gwani ne wajen bankado labari, yau da ganin na Ikara yace ‘dan uwana zuciyata tana yawan kai komo akan wani lamari, saboda yadda naga kasata na yawan mai da mai doki kan kuturi, Na Ikara yace a a dakata ‘Dan Iya kada ka jefani cikin dogon nazari, saboda na ‘kagara ka fitar min da komai sarari.

‘Dan Iya yace, gani kawai nayi duk lokacin da aka ce ga wani mukami da mata ke marari sai kaga manya kasarmu sun jefa babban buri, kokuma kaga sun shimfida wasu sharudda masu tsabar tsauri, saboda buri irin na mazan kasarmu sai dai ace kullum sune taurari, su kuwa mata idan suka yunkuro sai a buge su da bakin ban hakuri.

Na Ikara yace ‘Dan Iya naji batun ka amma yanzu sai ku godewa Allah tun da yanzu ance akwai macen da ta yunkuro fili tace ta gaji da jira, saboda a karon farko kasarka ta sami macen da ta fita filin gwagwarmayar taka takara. ‘Dan Iya yace Eh, nima naji dadin yadda aka sami macen data sha aradun wucewa gaba don yin shara, domin kuwa duk da irin ruwan suka da sakaka larura, Hajiyar Taraba ta nunawa duniya ta ‘darma tsara, amma kuma kash duk da haka naga wasu nata gabza mata sara, saboda mai makon a bar gaskiya ta yi aiki kowa ya fito fili a kara, wasu na ta kokarin ganin sun yi mata wasan kura. Kamar dai yadda yanzu komai ya fito fili karara, sai dai duk da haka mun san zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana Muzuru ana Shaho sai ya tsira.

Na Ikara yace Eh ‘Dan Iya kafadi gaskiya don yana da kyau musani cewa suma mata fa suna da ‘yan ci, a maimakon ace kullun bamu da aiki sai na nuna musu banbanci, wani lokaci ma ayi ta yaba musu muzanci shiyasa wasu da anyi maganar mata sai suce sun fiye lalaci, idan suka fito neman hakkin su ma sai ka ga ana ta dogon turanci, saboda su mata an sansu da kawaici saboda haka yasa nake ganin idan ana so mu fatattaki ha’inci mu kuma karya lagon tumasanci, sannan mu ‘daura damarar yaki da talauci to dole ne mu ‘daura mata don sun yi suna wajen karya zalunci.

‘Dan Iya yace to Allah dai yasa mu gane gaskiya gaskiyace muriketa, mu kuma gane baiwa daga Allah ce kuma yayi wa mata, shiyasa idan muna son kasarmu ta wadata har muyi sa’a ta baiwa saura rata, to wajibi ne idan mata suka zo da wata bukata, kokuma akace ga wawani mukami azo a nema, suka fito don su fafata to mu basu dukkanin goyon baya har burinsu ya tabbata, idan sunyi wani abin arziki kuma mu yayata, saboda idan akace matan kasar mu sun sami dukkan gata shikenan kasarmu zata tsira daga tarkon tatata.

XS
SM
MD
LG