'Yan Sama Jannati 3 Sun Dawo Daga Duniyar Wata

‘Yan sama jannatin kasa-da-kasa su uku sun dawo daga wani aiki da suka kwashe watanni 5 da rabi a duniyar wata, inda suka sauka a wannan duniyar a tsakanin kasar Rasha da kasar Kazakhstan, aikin da ya hada da gyaran mutun mutumi da aka aika duniyar ta wata.

Ma’aikatan biyu Amurkawa da dan kasar Rasha daya, sun sauka a yankin Soyuz jimkadan bayan ketowar alfijir a kasar Kazakhstan yau da safe, sun sauka cikin matsanancin yanayi mai tsabar sanyi.

Jirgin nasu ya samu sauka da ker, duk kuwa da iska mai karfi na kadawa, a cewar hukumar NASA sun sauka duk da tsammanin da akayi na cewar karfin iskar bazata basu damar iya saukaba.

Ma’aikatan hukumar ta NASA Joe Acaba da Mark Vande Hei, sai dan kasar Rasaha Alexander sun sauka daya bayan daya, suna dariya da daga hannun ga sauran jama’a, saukar su keda wuya jami’an kiwon lafiya suka rufesu cikin manyan barguna, aka kuma basu duk kulawa da ta kamata.

Yanzu haka dai sauran ‘yan sama jannatin uku na cikin duniyar wata don cigaba da aikin bincike.