Nishadi Tare Da Ibrahim Mai-shinku

Ibrahim Mai-shinku

A shirinmu na nishadi a yau ma ,na mussaman ne domin mun lalubo jarumi Ibraim Mai-shinku wanda masu kallo suka shafe tsawon lokaci basa ganinsa a akwatin talabijin dinsu

Ibahim Mai-shinku ya ce yana nan daram yanayi ne na rayuwa amma ya dawo da shirye shiryensa domin fito da wasu fina-finai masu kayatarwa da fadarkawa

Ya ce a tsawon lokacin da yayi ba’a ganinsa a akwatin talabijin ya je neman ilimi ne domin ya inganta harkar sa ta fim

A fannin tsegumi kuwa jarumai masu tasowa ,yan tagwaye Hasana da Husaina Musa sun dawo daga jihar Imo inda suka je bisa gayyatar gwamna Rochas Okorocha ya yi musu.