Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Wasu 'Yan Mata Akan Yadda Zasu Kauce Ma Matsalolin Da Ke Haddasa Rabuwa Da Masoyan Su


Kamar yadda muka ji ra'ayoyin wasu samari da dama, haka ma dandadalinvoa ya karkata akalar shirin inda muka yi kokari jin ta bakin 'yan mata akan abubuwanda zasu kaucewa domin gudun matsalolin da kan iya haifar da rabuwa da abokan soyayyar su.

Yawancin samari dai sun koka ne akan yadda kwadayi da karya ke ruruta wuta ko haifar da matsalar da yawancin lokuta kan haifar da rabuwa da masoya, 'yan matan sun koka ne akan kwadayin kayan duniya da kudi da kuma dogon burin da yawancin su ke sawa a zukatan su.

Idan mai karatu bai manta ba, wasu daga cikin samarin sun bayyan yadda wasu daga cikin su ke hangen kitse ga rogo, wato abinda suke tunani ko hange ba shi suke samu ba daga karshe, haka ma 'yan matan suka bayyana cewa hangen jin dadin da suke a wurin wasu maza na sa su auri mayaudara.

saurari cikakkiyar hirar a Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG