Jiragen Saman Leken Asiri Na Amurka Su Na Farautar Inda Aka Boye Daliban Chibok Da Kuma 'Yan Bindiga - 15/5/2014

Jirgin leken asiri maras matuki na hukumar kwastam ta Amurka

Sakataren tsaron Amurka, Chuck Hagel, yace Amurka tana amfani da jiragen saman leken asiri marasa matuka a ciki, wajen farautar inda 'yan bindiga suka boye dalibai mata su fiye da 270 da suka sace a Najeriya.

Hagel ya fadawa 'yan jarida a Sa'udiyya wajen wani taron kasashen yankin Gulf cewa a yanzu, jiragen saman leken asiri na Amurka su na shawagi a samaniyar Najeriya.

Yace, "jiragen marasa matuka na Amurka zasu rika shawagi a samaniyar Najeriya tare da wani jirgin saman leken asiri mai matuki a ciki, a wani bangare na yunkurin da ya hada da wasu kwararru su kimanin 24 da Amurka ta tura Najeriya domin taimakawa kasar wajen gano inda aka boye daliban."