Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Ga Diyata Cikin Bidiyon 'Yan Boko Haram In Ji Wani mahaifi dan Chibok - 13/5/2014


Mahaifin daya daga cikin ‘yan mata kusan 300 da aka sace a Najeriya yace ya gane diyarsa a cikin faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar. A hirar da yayi da DandalinVOA dazun, wannan mahaifin yace ya ga diyarsa mai shekaru 18, da kuma wata mai kama da diyar makwabcinsa a cikin wannan faifan bidiyo.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:49 0:00
Direct link

A halin da ake ciki dai, Amurka ta ce jiragen leken asirinta sun fara shawagi a wannan yanki, kuma zata tura irin jiragen nan marasa matuka wadanda zasu iya sunsuna duk inda mutum yake cikin daji daga can sama, ko dare ko rana.
XS
SM
MD
LG