Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubakar Shekau Na Gaskiya Fa Ya Mutu, Wannan Dan Jebu Ne - In Ji SSS - 12/5/2014


Hoton Abubakar Shekau daga bidiyon da kungiyar Boko haram ta bayar litinin 12 Mayu, 2014.
Hoton Abubakar Shekau daga bidiyon da kungiyar Boko haram ta bayar litinin 12 Mayu, 2014.
Kakakin hukumar tsaron ciki gida ta SSS a Najeriya, Marilyn Orgar, ta ce Abubakar Shekau na ainihi wanda ya taba zama mukaddashin Muhammadu Yusuf, ya kuma zamo shugaban kungiyar Boko Haram daga baya, ya mutu, kuma wanda yake nuna kansa yanzu a zaman Abubakar Shekau dan jebu ne yayi shigar burtu.

A lokacin da take amsa tambayar da wakiliyarmu Madina Dauda ta yi kan kalamunta na cewa abubakar Shekau da Abu Qaqa sun mutu, Marilyn Orgar ta ce, "Madina, bari na fada miki a fili cewa Boko Haram, kungiya ce da kowa ke fakewa karkashinta ya ce shi ma ita ce. Kuma da yake kowa zai iya fakewa da ita, kowa zai iya sanya ma kansa duk sunan da yake so."

Ta kara da cewa, "Mutumin da yake nuna kansa a zaman shugaban Boko Haram, ya sanya ma kansa ne sunan Shekau, Abubakar Shekau. Amma (Abubakar) Shekau na asali ya mutu."

Marilyn Orgar ta ce "lokaci bai yi ba da zan fito in bayyana dalilan da suka sanya na fadi hakan, domin mun san shi (wanda yake kiran kansa Shekau din) kuma ya san mu. Don haka, wannan mutumin da ake gani ba Abubakar Shekau ba ne."

Ta ce yanzu kungiyar Boko Haram ta koma wata dabam, ana amfani da ita domin fashi da yin wasu abubuwan da dama, don haka ta zamo wadda kowa zai iya kwaikwayonta.

Ta ce ni ma ina iya farkawa gobe in ce ni 'yar Boko Haram ce in fara cin zarafin mutane.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:51 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG